1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lafiya Jari: Zagaye na uku na corona a Afirka

Abdourahamane Hassane
April 16, 2021

Likitoci da kwarraru na ci gaba da fadikar da al'umma a Najeriya game da karbar aLlura riga kafi ta yaki da annobar corona a wasu wuraran jama'a na karba wasu kuma ba sa karba.

https://p.dw.com/p/3s6oL
AstraZeneca Covid-19 Impfung
Hoto: NurPhoto/picture alliance

Yanzu haka dai a kasashe dabam-dabam na duniya ana ta kokarin samar a alluran rigakafi na yaki da cutar corona wanda tuni a kasashe da dama aka soma yin allurar wa jama'a. Najetriya na daya daga cikin kasashen da suka samu alluran rigakafin na baya- bayan daga Indiya sama a allurar dubu 100 karin wadanda ake da su wanda aka soma yi wa al'umma. Rigakafin wani abu ne da zai iya kare jama'a ga takayara ko ma rasa rai inda har aka harbu da corona saboda ko za ta zo da sauki idan har aka yi allura sabannin wanda bai yi ba, sai dai jama'a na yin dari-dari.