Labarin Wasanni: 01.02.2021 | Zamantakewa | DW | 01.02.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Labarin Wasanni: 01.02.2021

Za mu ji inda aka kwana a wasannin neman cin kofin kwallon kafa na matasa na Afirka da ke wakana a Kamaru, akwai kuma sakamakon wasannin Bundesliga da aka gudanar a karshen mako.

Deutschland Bundesliga Borussia Dortmund - FC Augsburg | Tor Sancho

Fafatawa tsakanin Dortmund da Augsburg

A wasannin Bundesliga da aka fafata a karshen mako, Stuttgart ta lallasa Mainz ta ci biyu da nema. Bayern ma ta yi wa Hoffenhieim cin kaca hudu da daya yayin da wasa tsakanin Eintracht Frankfurt da Hertha Berlin aka tashi uku da daya. Unioin Berlin ta yi kunnen doki da Shake 04 da ci daya da daya Lepzig kuma ta lallasa Bayer Leverkussen da ci daya mai ban haushi, kana an tashi tsakanin Borussia Dortmund da Augsburg ci uku da daya.

Kamaru da Mali da Guinea da kuma Maroko sun tsalleke zuwa matakin daf da na karshe a gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka na matasa masu tamaula a gida wato CHAN. A wasannin tennis shahararriyar 'yar wasan ta Amirka Serena Williams ta fara shekarar da kafar dama inda ta doke Daria Gavrilova da ci  shida da daya da kuma shida da hudu a wasan da ya gudana a birnin Melbourne na kasar Ostreliya, yayin da ake shirin fara daya daga cikin wasannin Tennis masu tasiri na duniya wato Australian Open daga ranar takwas ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki zuwa 21 ga watan na Fabarairun.

 

Sauti da bidiyo akan labarin