1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kyakkyawar fata ta samun ci gaba a fannin noma

Uwais Abubakar Idris
August 28, 2019

A Najeriya kwararru a harkar noma sun ce har yanzu akwai jan aiki wajen kyautata harkar noma don samar da karin kudadden shiga ga kasar

https://p.dw.com/p/3OeR4
Nigreria Fulani-Nomaden
Hoto: AFP/Luis Tato

Tsawon kwanaki biyu masanan a fanoni daban daban na aikin gona suka kwashe suna tattaunawa kama daga yanayin kasar noma da irin shuka, da yadda ya kamata a gudanar da noman don samun albarka da ma hanyoyin adana kayan noman domin samun riba.

Ko da yake an samu ci gaba a harkar noma a Najeriya daga 2015 da gwamnatin ta mayar da hankali a kan lamarin, a cewar Dr Almujtaba Abubakar Gumi mataimakin shugaban cibiyar ‘yan kasuwa ta Abuja akwai jan aiki sosai a kan mayar da harkar noma kasuwancin da zai taimaka wa tattalin arziki.

eco@africa Zero-waste farming in Nigeria
Hoto: DW

Masanan sun kuma tabo batun rawar da aikin noman ke takawa wajen samar da ayyukan yi ga matasan Najeriya ba kawai a yankunan karkara ba har ma ‘yan Boko sun rungumi harkar. 

Sai dai ganin har yanzu fannin noman na samar da kashi 21 ne kacal ga tattalin arzikin Najeriya ya sanya masana nuna damuwa abinda Malam Abdullahi Ringim shugaban kungiyar masu noman tumatir yace akwai gyara ga yadda aka tsara manufofin.

Dr Baba Ashmara na hukumar kasar Jamus da ke bada taimakon raya kasa watau GIZ ta bullo da sabon tsari na noman zamani da baya lalata muhalli.

A nasa bangaren Mr Martyn Daimond Black jami’in shirin bunkasa noma a Afrika da suka shirya taron, yace ilimi da wayar da kan da aka samu ya nuna kyakkyawar fata ta samun ci gaba a fannin noma.