1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An kamalla binciken asalin corona

Ramatu Garba Baba
February 10, 2021

A wannan Larabar ce tawagar kwararru ta Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da kamalla binciken asalin corona da ya kai ta garin Wuhan na kasar China.

https://p.dw.com/p/3pBex
China Wuhan | Coronavirus | PK der WHO zu Untersuchungen
Hoto: Aly Song/REUTERS

Tawagar Hukumar Lafiya ta Duniya da aka tura birnin Wuhan na China don gudanar da binciken corona, ta baro kasar a wannan Laraba, bayan ikirarin samun bayanan da suka je nema a game da asalin cutar. Jagoran tawagar Peter Daszak , ya ce, yanzu sun gano inda aka dosa a game da musababbin cutar dama tabbatar da asalinta.

Tun dai bayan bullar cutar corona a Disambar 2019, ake zargin cewa, cutar ta bulla bayan sakaci na barin yoyon wani sinadari a dakin gwaji a Wuhan, akwai masu cewa an yada cutar bayan cin naman jemage da ake siyarwa a wata kasuwa a Chainan da dai sauransu, batun da gwamnatin Chainan ta sha musawa. 

Ana fatan ganin wannan binciken na Hukumar Lafiya zai taimaka kwarai a gano bakin zaren warware takaddama kan annobar corona da kawo yanzu tayi sanadiyar rayuka sama da miliyan biyu tare da durkusar da tattalin arzikin duniya.