Kwararru sun bukaci rage dumamar duniya | Labarai | DW | 17.06.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwararru sun bukaci rage dumamar duniya

Shugabar hukumar kula da sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya Patricia Espinosa ta jaddada bukatar rage dumamar duniyar da maki daya da rabi a ma'aunin Celcius yayin taron duniya kan sauyin yanayi a birnin Bonn.

Jakadu da kwararru kan sauyin yanayi daga sassa daban daban na duniya sun fara gudanar da babban taro a birnin Bonn kan sauyin yanayi a daidai lokacin da ake kara matsin lamba kan gwamnatoci su gaggauta daukar matakan shawo kan dumamar duniya.


Jami'ai da ke halartar taron wanda za a shafe kwanaki goma ana yi sun mayar da hankalinsu ne kan yadda za a warware matsalolin da aka kasa cimma daidaito akan su a taron sauyin yanayin da ya gudana a watan Disambar bara a kasar Poland.


Matsalolin sun hada da dokoki da suka shafi cinikin hayakin masana'antu wanda zai baiwa kasashe masu arziki damar daidaita hayakin da suke fitarwa ta hanyar biyan kudin aiwatar da wasu muhimman ayyauka a kasashe matalauta.


Da take jawabi shugabar hukumar kula da sauyin yanayin Patricia Espinosa ta jaddada bukatar rage dumamar duniyar da maki daya da rabi a ma'aunin Celcius 


"Lokaci ya yi da dukkan jama'a za su bude idanuwansu kan yadda lamuran ke bukatar kulawar gaggawa. Babu wani sarari na bata lokaci."


Espinosa wadda tsohuwar ministar harkokin waje ce ta kasar Mexico ta yabawa Greta Thunberg wata yarinya yar fafatuka ta kasar Sweden da kuma dubban dalibai a fadin duniya wadanda suka bi sahu wajen yin tattaki jawo hankali kan sauyin yanayin muhalli a duniya.