Kwamitin Nuhu Ribadu ya mika rahotonsa | Siyasa | DW | 02.11.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kwamitin Nuhu Ribadu ya mika rahotonsa

Abin kunyar sace kudaden rarar man fetur da gas a Najeriya ya dauki hankali a daidai lokacin da kasar take fafitikar yaki da cin hanci da rashawa

A yau ne shugaban kasa Jonathan Goodluck ya karbi kundin dake dauke da rahoton da wakilan wani kwamiti suka mika masa, wanda gwamnatin taraiya ta kafa, domin bincike da gabatar dfa shawarwari a game da madakalar almubazzaranci ko sama da fadi da kudi mai yawa daga rarar man fetur da kasar take da arzikinsa. Wannan kwamiti da aka sani da sunan kwamitin Ribadu, ya nuna cewar wannan abin kunya shine mafi tsanani a kasa kamar Najeriya mai dimbin arzikin man fetur, amma wasu mutane ne yan kalilan suke abin da suka so da dukiyar da kasar take samu daga wannan arziki nata.

Tuni dai ake ta baiyana radi-radi a game da abin da rahoton ya kunsa da kuma wadanda aka ambace su cikin wannan abin kunya na sace kudaden rarar kudin na man fetur da gas. Wakilinmu a Abuja, Ubale Musa ya sami shi kansa shugaban kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa, wato Mallam Nuhu Ribadu, inda yayi hira dashi domin jin karin haske a game da abin da rahoton ya kunsa da da dalilan da suka sanya ya zama tilas a kafa wannan kwamiti.

Mawallafi: Umale Musa
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin