1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwalara ta yi barna a Zimbabuwe

September 12, 2018

Hukumomin lafiya a Zimbabuwe sun tabbatar da bullar cutar kwalara a Harare babban birnin kasar, bayan cutar ta halaka akalla rayukan mutane 20.

https://p.dw.com/p/34iRa
Zimbabwe Cholera Patienten
Hoto: AP

Bayanan hukumomin na lafiya, sun ce baya ga mutanen 20 da suka mutu, akwai ma wasu sama da 2000 da aka hakkake sun kamu da kwayar cutar sakamakon shan gurbataccen ruwa.

Jami'an ma'aikatar da ke kula da birnin, sun ce cikin shekaru sama da goma da suka gabata, sun yi kokarin sama wa mazauna wasu yankunan da ke kewayen Hararen ruwa mai tsafta, sai dai hakan bai yiwu ba.

Ko a shekara ta 2008 ma dai kasar ta Zimbabuwe ta yi fama da wani bala'in cutar ta kwalara, inda sama da mutum 4000 suka salwanta, wasu kimanin dubu 40 su ne aka yi nasarar yi wa magani.

Cutar dai na shafar harkokin tattalin arziki a kasar.