Kwace mahakar man fetur a Libiya | Labarai | DW | 04.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwace mahakar man fetur a Libiya

Wasu 'yan bindiga da ake zargin suna da alaka da kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta kasar Libiya sun kai wani mummunan hari tare da kawace iko da mahakar man feturn din kasar.

A cewar mahukuntan kasar ta Libiya wannan harin na zaman na biyu mafi muni da aka kai cikin mako guda. Wata majiya da ga ma'aikatar diplomasiyar kasar Faransa da ke birnin Pari ta bayyana cewa ana zargin ma'aikatan wajen guda hudu sun rasa rayukansu a yayin harin da aka kai a mahakar man fetur din da ke yankin al-Mabrook a kudancin garin Sirte. Kasar Libiya dai ta shiga halin rudani tun bayan da aka kifar da gwamnatin marigayi tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi a yayin juyin-juya halin kasar a shekara ta 2011.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu