Kuri′ar raba gardama a Burundi ta dau hankalin jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 18.05.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Kuri'ar raba gardama a Burundi ta dau hankalin jaridun Jamus

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi tsokaci kan kuri'ar raba gardama da aka gudanar ranar Alhamis a kasar Burundi. Berliner Zeitung kuwa ta yi tsokaci kan annobar Ebola a Kwango.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce a Burundi shugaban kasa Pierre Nkurunziza ya bari an gudanar da wata kuri'ar raba gardama kan yi wa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima da zai ba shi damar ci gaba da mulki har shekarar 2034.

Sannan a lokaci guda rikici ya rincabe. Hasali dai a shekarar 2015 wa'adin mulkin Shugaba Nkurunziza da ke kan mulki tun a 2005 ya kare bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki.  A shekarun baya-bayan nan shugaban ya yi ta gudanar da mulki na kama karya musamman tun bayan da sojoji suka yi yunkurin juyin mulki a shekarar 2015 saboda shirya zabe karo na uku da Nkurunziza ya yi, abin da ya sabawa kundin tsarin mulki. Su kuma 'yan adawa suka samu kwarin gwiwa. Dakarun tsaro da 'yan bangar siyasa na kungiyar matasan jam'iyyar da ke jan ragamar mulki, suka yi ta farma ‘yan adawa suna halaka su. Mutane 1200 suka rasa rayukansu a rikice-rikicen na tsawon shekaru ukun da suka wuce yayin da dubbai ne suka tsere zuwa makwabciyar kasa Tanzaniya. Yanzu haka ana fargaba dangane da yiwuwar kazancewar rikicin da ke tuni da yakin basasar da Burundi ta yi fama da shi a shekarun 1990.

Shirye-shiryen ko-takwana tun ba a shiga mummunan hali ba inji jaridar Berliner Zeitung, tana mai cewa a kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango annobar cutar Ebola ta sake barkewa, a saboda haka hukumar lafiya ta duniya WHO ta fara daukar matakan hana bazuwar cutar musamman a yankin Arewa maso Yammacin Kwangon inda cutar ta barke.

Jaridar ta ce yanzu haka dai an tabbatar da mutuwar akalla mutane 20 daga cikin mutum fiye da 40 da suka kamu da ita. Kasancewa cutar ta bulla a wani yanki da ke cikin kungurmin daji inda ba hanyoyin mota ko wani fili da jirgin sama zai iya sauka, a dole ana amfani da jirgin sama mai saukar ungulu wajen jigilar likitoci da sauran masana na hukumar WHO zuwa yankin.

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel a wannan makon labari ta buga dangane da sarrafa kofi da cokulet da ake yi a Afirka zuwa Turai, abin da jaridar ta ce yana kan turbar da ta dace.

Ta ce samar da cokulet a Afirka wannan shi ne tunanin wani Bature mai suna Hendrik Reimers cewa kasashen Afirka za su fi samun riba idan suka shigo da kayayyakin da aka sarrafa maimakon danyun a nahiyar Turai. Yanzu haka Hendrik Reimers wanda ya taba aiki da kamfanonin fasahar sadarwa na SAP da IBM ya kafa wani kamfani a birnin Munich na nan Jamus mai suna Fairafric wato mai ma'ana adalci ga Afirka. Ya samu wani kamfani a Ghana da suke kawance. Kamfanin Fairafric daya ne daga cikin kamfanoni da ke son a sanya adalci a huldar ciniki da kasashen Afirka.