Kurdawan Siriya sun aikata manyan laifukan yaki | Labarai | DW | 13.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kurdawan Siriya sun aikata manyan laifukan yaki

Kungiyar Amnesty International ta zargi mayakan Kurdawa na kasar Siriya masu samun goyon bayan Amirka, da aikata manyan laifukan yaki a garuruwan da suka kwace.

Kungiyar dai ta zargi Kurdawan na Siriya da cin zarafin wadanda ba kurdawa ba tare da kone musu gidaje kurmus. A cikin wani rahoto ne mai shafuka 38 kungiyar mai kula da kare hakin dan Adam ta Amnesty International, ta ce ta tattauna da mutane kusan 40 da dukanninsu suka fuskanci mumunar muzgunawa daga mayaka na Kurdawa a garuruwan Rakka da Hassaka, bisa zarginsu na cewa suna da alaka da 'yan kungiyar IS. A cewar Lama Fakih mai ba da shawara a kungiyar ta Amnesty International, hukumomin na Kurdawa ko kadan ba sa mutunta dokokin kasa da kasa kan hakkin dan Adam.