Kurdawan Iraki sun karbe iko da Kobani | Labarai | DW | 26.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kurdawan Iraki sun karbe iko da Kobani

Kurdawan Iraki da ke samun taimakon sojin Amirka a yakin da ake yi 'yan kungiyar nan ta IS sun samu nasarar fattatakar 'yan IS din daga garin Kobani da suke rike da shi.

Hukumar nan ta kare hakin bani Adama ta Syrian Observatory for Human Rights da ta tabbatar da wannan labarin ta ce an tafka kazamin fada kafin kaiwa ga samun wannan nasara kuma a halin da ake ciki babu mayakan na IS a garin baki daya.

A watan Yulin shekarar da ta gabata ne kungiyar ta IS da ke rajin kafa daukar Islama a Siriya da Iraki ta karbe iko da garin na Kobani kafin daga bisani kawancen sojin Amirka da na wasu kasashen Larabawa su fara kai musu farkmaki da nufin dakile aiyyukansu.