1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Najeriya: Shirin kafa majalisa ta 10

Uwais Abubakar Idris
June 9, 2023

Majalisar dokoki ta 10 na kara dagewa na nema wa kanta ‘yancin a zaben wadanda za su zama shugabanin majalisar da za a kaddamar a makon gobe.

https://p.dw.com/p/4SP4F
Nigeria Politik l Senat
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Majalisar dokoki ta 10 a Najeriya na kara dagewa wajen neman 'yancin kanta a zaben wadanda za su zama shugabanin majalisar da za a kaddamar a makon gobe, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke kara dagewa a sanya mutanen da take so su jagoranci majalisar. Kura dai na kara tirnikewa a kan  wannan batu na neman shugabancin majalisar dokokin Najeriya ta 10, inda 'yan majalisar ke nuna cewa ko wayo fa ya san na ki a kan abin da suka kira kokarin yi masu karfa-karfa a kansu wadanda za a nada a matsayin shugabaninsu. Ta kai ga shugaban Najeriyar ganawa da 'yan majalisa a mataki na neman goyon baya, tuni dai ta bayyana a fili jam'iyyar APC mai mulki da ma bangaren shugaban Najeriyar Bola Ahmed Tinubu suka nufa a kan wannan batu na shugabannin majalisar, domin kuwa inda baki ya karkata nan yawu ke zuba.

Sun kai ga fitowa fili suna bayyana sunayen mutanen da suke son a zaba, koda yake jam'iyyar ta dage kan cewa shawara ta bayar. Duk da cewa tsari ko salo da ke neman zama abin da aka saba da shi na Najeriyar, domin tun daga 1999 jam'iyya da ke mulki ke nuna mutanen da za a zaba a majalisar domin samun goyon baya da saukin tafiyar da mulki. A yanzu da ya rage 'yan kwanaki kalilan a kaddamar da majalisa ta 10, tuni ake kashedin abin ka iya faruwa idan jam'iyya mai mulki da fadar shugaban Najeriya suka ci gaba da dagewa. Ana ci gaba da kamun kafa tsakanin masu goyon bayan 'yan takarar da jam'iyyar APC ta fitar da 'yan majalisar da ke dagewa kan ba su yarda a yi musu dauko dora a shugabanin da za su jagorance su a majalisar ba.