Matsalar yawan yara cikin bakin haure
October 30, 2025
Wani saurayi dan shekara 15 da ya fito daga Guinea Conakry, na daga cikin wadanda kungiyar SOS Humanity ta ceto a tekun Bahar Rum, a lokacin da yake yunkurin shiga Turai ba tare da rakiya wani mutum da ya mallaki hankalin kansa ba.
Bayanin halin da ake ciki
Ita wannan kungiya mai zaman kanta da ke da mazauna a birnin Berlin na Jamus, ta shafe shekaru goma tana ceto bakin haure da ke neman nutsewa a teku. Saboda haka ne ta ja hankali kan yawan yara da matasa da ke shiga kwale-kwalen da ke cike da mutane daga Libya ko Tunisiya, inda ta ce kusan kashi daya cikin biyar na wadanda aka ceto yara kanana ne.
Esther, da ta ce a sakaye sunanta, kwararriyar masaniyar ilimin halayyar dan adam, ta yi aikin sa kai a matsayin jami'ar kula da lafiyar kwakwalwa a jirgin ceto na Humanity 1 a watan Nuwamba da Disamba 2024. Ta ba da labarin cewa kwale-kwale shida dauke da mutane 347 suka ceto su, kuma daga cikinsu akwai yara kanana 43, galibi matasa marasa rakiya a yanaqyi na raunin jiki da tunani.
Libiya tana cikin hanyoyin masu hadari
Masu karancin cikin sahekaru na cikin mummunan hali a sansanonin da ke tsugunar da su a Libiya, kasar da ke fuskantar suka mai tsanani kan take hakkin bakin haure ta hanyar cin zarafi da azabtarwa, da fataucinsu. Sai dai, idan yara da matasan da ke neman tsallakawa Turai suka samu damar tserewa daga sansanonin, suna fuskantar hadarin rasa rayukansu.
Kiyasin da Asusun Yara ta UNICEF ta yi daga watan Afrilun 2025, ya nunar da cewar kimanin yara da matasan Afirka 3,500 sun mutu ko sun bace a cikin shekaru goma da suka gabata yayin da suke kokarin isa Italiya ta hanyar tsallaka Bahar Rum. Wannan yana nufin cewar yaro daya na mutuwa ko yana bacewa a kowace rana a tsawon shekaru goman da suka gabata. Saboda haka ne kungiyar SOS Humanity ta yi kira da a kawo karshen hadin gwiwar Kungiyar Tarayyar Turai da Libya da Tunisiya.
Rushewar USAID yana da mummunan sakamako
Matsalar da yara da matasa da ke neman zuwa Turai ta barauniyar hanya na iya ta'azzara a nan gaba, in ji Lanna Idriss, Shugaba na SOS Children's Villages, bayan da gwamnatin Amurka a karkashin Shugaba Donald Trump ta rusa hukumar ba da agajin ta USAID.