1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyoyi za su tallafa wa 'yan Syria

April 26, 2018

Kungiyoyin agaji na duniya sun yi alkawarin samar da makudadan kudade don agaza wa 'yan gudun hijiran da ke Syria da wasu kasashen yankin da ke fama da yaki.

https://p.dw.com/p/2wjAu
Jordanien syrische Flüchtlinge in Trabeel
Hoto: picture alliance/dpa/AP Photo/R. Adayleh

Kungiyoyin agaji na duniya sun yi alkawarin samar da dala biliyan 4 da miliyan 400 don agaza wa 'yan gudun hijiran da ke Syria da kasashe makwabta da ke fama da yake-yake. Kudaden dai kamar yadda alkaluma suka nunar, sun gaza adadin abin da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukata, don daukar nauyin masu hijirar na Syria a bana kadai.

Akwai sama da mutum miliyan 13 da ke cikin bukatar dauki a Syria, yayin da ake da wasu 'yan kasar da ke fakewa a kasashen Labanan da Jordan da kuma Turkiyya. A bara, bankin duniya ya yi kiyasin asarar da Syria ta yi cikin biranen Aleppo da Damascus da kuma birnin Homs, da cewa ta kai na dubban biliyoyi na dalar Amirka.

Majalisar ta Dinkin Duniya dai, ta ce an kamo hanya, da wadannan alkawura da kungiyoyin na duniya suka yi.