Kungiyar tsrao ta NATO tana taro kan kasar Turkiya | Labarai | DW | 28.07.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar tsrao ta NATO tana taro kan kasar Turkiya

NATO ta ce Turkiya ba ta gabatar da neman karin taimako ba kan yaki da 'yan ta'adda

Kungiyar tsaro ta NATO-OTAN ta bayyana goyon baya ga kasar Turkiya kan yaki da ta'addanci, bayan da kasar ta Turkiya ta kira taron gaggawa na kungiyar a birnin Brussels na kasar Beljiyam. Mahukuntan birnin Ankara sun kira taron bayan kaddamar da hare-hare da tsagerun kungiyar IS da ke neman kafa daular Islama a Siriya da kuma 'yan awaren Kurdawa.

Kasar ta Turkiya ba ta nemi karin taimako ba daga kungiyar ta NATO. Shugaban jam'iyyar HDP da ke goyon bayan Kurdawa da Shugaba Tayyip Erdogan ya zarga da nasaba da 'yan ta'adda ya musanta yin ba daidai ba, inda ya ce ana hukunta su ne saboda nasarar da suka samu lokacin zaben da ya gabata.