Kungiyar Taliban ta kai hari a birnin Kabul | Labarai | DW | 28.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Taliban ta kai hari a birnin Kabul

Mutum daya a yayin da akalla wasu 13 suka jikkata dukkaninsu farar hula a cikin wani harin kunar bakin wake da Taliban ta kai da mota a wannan Litinin a kusa da filin jiragen saman birnin Kabul.

Hukumomin kasar Afganistan sun tabbatar da mutuwar mutum daya a yayin da akalla wasu 13 suka jikkata dukkaninsu farar hula a cikin wani harin kunar bakin wake da kungiyar Taliban ta kai da mota a wannan Litinin a kusa da filin jiragen saman birnin Kabul.

Wani babban jami'in ministan cikin gida na kasar ta Afganistan Najib Danishe ya bayyana cewa harin an kai shi ne kan ayarin sojojin kungiyar tsaro ta NATO ko OTAN da ke a birnin. Tuni dai a shafinsa na Tweeter Kakakin kungiyar ta Taliban Zabiullah Moudjahid ya dauki alhakin kai wannan hari.

A makon da ya gabata ma dai sojojin Amirka shida sun halaka a cikin wani harin kunar bakin waken da wasu 'yan bindigar suka kai a kusa da barikin sojan Bagram ta arewacin birnin na Kabul.