Kungiyar NATO ta nuna damuwa da Rasha | Labarai | DW | 23.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar NATO ta nuna damuwa da Rasha

Rasha ta ce tana mutunta dokokin duniya kan jibge dakaru kusa da iyakarta da Ukraine. Tuni dai dakarun kasar suka kwace sansanin sojin Ukraine da ke Krimiya.

Ma'aikatar tsaron kasar rasha ta bayyana cewa tana kiyayewa da dokokin kasashen duniya kan yawan dakarunta kusa da iyaka da kasar Ukraine, sakamakon yadda kungiyar tsaro ta NATO ta nuna damuwa da yawan sojojin da Rasha ta jibje.

Dakarun kasar ta Rasha sun kwace sansanin sojin saman Ukraine cikin yankin Krimiya. Matakin ya zo kwana guda bayan Shugaban Rasha Vladimir Putin ya saka hannu kan yarjejeniyar da ta hade yankin na Kiriya da kasar ta Rasha.

Tun farko dakarun na Ukraine sun yi fice daga wani sansanin sojin ruwa da masu goyon bayan Rasha sun mamaye.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar