Kungiyar NATO da dakarun Afghanistan sun kashe ´yan tawaye 150 | Labarai | DW | 11.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar NATO da dakarun Afghanistan sun kashe ´yan tawaye 150

Kungiyar tsaro ta NATO ta ce ta halaka mayakan Taliban su kimanin 150 a wani gumurzu da suka fafata a gabashin Afghanistan. A cikin wata sanarwa da ta bayar NATO ta ce an ga lokacin da mayakan suka hadu a Pakistan kuma suka tsallake kan iyaka kafin su kai wani hari. Dakarun NATO da takwarorin su na Afghanistan sun mayar da martani ta amfani da bindigogin atileri da kuma jiragen saman yaki. Da farko ma´aikatar tsaron Afghanistan ta ba da kiyasin halaka ´yan tawaye 80. Kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da yawan ´yan tawayen da aka kashe a gumurzun wanda aka yi a lardin Paktika dake kusan da kan iyakar Afghanistan da Pakistan.