1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar IS ta sake kashe wani dan Japan

Mouhamadou Awal BalarabeFebruary 1, 2015

Kungiyar da ke da kaifin kishin addinin ta sanya faifan bidiyo na kisan yankar rago da ta yi wadan jaridar kasarJapan Kenji Goto a kafar sadarwa ta Internet.

https://p.dw.com/p/1EU1D
Hoto: Social media website via Reuters TV

Kungiyar IS da ke gagwarmaya da makamai a Iraki da Syriya ta halaka wani dan jaridar kasar Japan da ta ke garkuwa da shi. A ranar Asabar da maraice ta sanya faifan bidiyon kisan yankar rago da ta yi wa Kenji Goto a kafar sadarwar ta internet. Wannan dai shi ne dan japan na biyu da masu kaifin kishin addini suka kashe a cikin mako guda.

Gwamnatin Japan ta bayyana takaicinta dangane da abin da ya faru. sai dai ta shan alwashin ci gaba da bayar da taimakon jin kai a kasashen Syriya da Iraki da ke fama da rikici. Sannan kuma ta ce ba za ta taba mika wuya ga bukutan wata kungiya ta ta'addanci ba.

Shugabannin kasashen Amirka da Faransa da kuma firaministan Birtaniya sun mikawa takwaransu na Japa sakon ta'aziya tare da yin tir da matakin Is na kashe wadanda ta ke garkuwa da su.

Idan za a iya tunawa 'yan kasashen yamma biyar ne kungiyar IS ta yi ikirarin kashewa cikin watanni shida na baya-bayannan ciki har da Amirkawa biyar da kuma jami'an agajin Birtaniya biyu.