Kungiyar IS babbar barazana ga duniya | Labarai | DW | 11.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar IS babbar barazana ga duniya

Wani rahoton na MDD ya ce kungiyar IS da Al Qaida, sun kasance da karfinsu na yin mugunta a cikin watanni shidda na farkon wannan shekara duk da irin taron dangin da ake yi musu.

Rahoton ya ce duk da irin matsin lamba da kungiyoyin suke fuskanta a Iraki da Siriya kungiyar IS har yanzu ta kan iya aikewa da kudade ga magoya bayanta na waje da ke a Yankin Gabas ta Tsakiyya. Haka kuma kungiyoyin na IS da Al-Qaida sun yi sayu a cewar rahoton na kwamitin sulhu na MDD a Afirka ta Yamma da ta Gabas da kuma a cikin kasashen Larabawa da Asiya ta Kudu.