Shugabannin kungiyar kasashe masu cigaban masana'antu na G7 sun cimma matsaya na kawo karshen amfani da makamashi kwal nan da shekarar 2035 a sanarwar da kungiyar ta fidda.
Sanarwar da Jamus da Birtaniya da Faransa da Italiya da Japan da Canada gami da Amirka suka fidda a karshen taronsu na kwanaki uku a Berlin, na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen yamma ke fuskantar barazanar tsadar makamashi a sabili da yakin da Rasha ke yi a Ukraine. Kuma suke neman sabbin hanyoyin rufe gibin makamashin da suke samu daga Rasha ruwa a jallo.
Jamus da ke zama shugabar kungiyar a yanzu haka ta ce a yayin da suke kokarin lalubo sabbin hanyoyi dole ne su lura da bukatar inganta muhalli.
Shugabannin kungiyar dai sun sha alwashin karkata ga makamashin da ake sabuntawa. A karon farko kungiyar ta G7 ta kuma sha alwashin taimakawa kasashe matalauta a saboda kalubalen da suke fuskanta kan sauyin yanayi.