Kungiyar Boko Haram ta fidda sabon bidiyo. | Labarai | DW | 15.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Boko Haram ta fidda sabon bidiyo.

Sabon faifan bidiyon ya nuna 14 daga cikin 'yan mata 'yan makarantar Chibok na Jihar Borno da kungiyar ta yi garkuwa da su a watan Afrilun shekara ta 2014.

Bisheriger Anführer der nigerianischen Miliz Boko Haram Abubakar Shekau (picture-alliance/AP Photo)

Abubakar Shekau shugaban kungiyar Boko Haram

Duk da cewa kawo yanzu ba a tantance lokaci ko inda aka nadi sabon bidiyon ba, amma bidiyon na tsawon mintuna 20 shine na farko a wannan shekarar bayan wani irinsa da kungiyar ta fitar a watan Mayun shekarar da ta gabata.

Bayan da shugaban kungiyar Abubakar Shekau rataye da bindiga ya yi jawabi na mintuna 13, guda daga cikin 'yan mata uku da aka gani dauke da jarirai a bidiyon ta ce mu ne 'yan matan Chibok kuma da yardar Allah ba zamu dawo gareku ba.

Kungiyar ta'adda ta Boko haram ta kame dalibai 276 daga makaratarsu a garin Chibok a watan Afrilun shekara ta 2014 lamarin da kasashen duniya suka yi Allah wadai.da shi.