Kungiyar Avengers ta sake fasa rijiyoyin mai a Najeriya | Labarai | DW | 01.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar Avengers ta sake fasa rijiyoyin mai a Najeriya

Tsagerun Niger Delta sun yi ikirarin kai hari kan rijiyoyin mai na kamfanin Chevron, a Jerin hare-haren baya bayan nan da ke kassara aikin hakar mai a Najeriya.

Tsagerun kungiyar Niger Delta Avengers a Najeriya sun ce sun kai harin bam a kan rijiyoyi biyu na kamfanin Chevron da ke a yankin mai arzikin man fetur. A sakon da ta wallafa ta Twitter kungiyar ta ce duk da kasancewar sojoji da kananan jiragen ruwa 100 da jiragen ruwan yaki hudu da kuma na sama, kungiyar NDA ta tarwatsa rijiyoyin mai na Chevron da sanyin safiyar wannan Laraba. Kawo yanzu jami'an kamfanin sun ki su ce uffan dangane da harin, amma wata majiyar masana'anta da ta ce a sakaya sunanta ta tabbatar da harin a kan rijiyoyin man guda biyu. Wannan harin shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da ya janyo koma baya ga aikin hako mai a yankin na Niger Delta.