Kungiyar AU ta bukaci Trump ya nemi gafara | Labarai | DW | 13.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar AU ta bukaci Trump ya nemi gafara

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ta yi Allah wadai da kalaman wulakanci da aka zargin shugaba Donald Trump ya aikatawa a kan kasashen Afirka da kasar Haithi hada da kasar El Salvador.

An dai zargi shugaba Trump da subul dan baka ne a yayin ganawarsa da masana harkokin shari'a domin tattauna yiwuwar sake kwaskwarima kan tsarin 'yan ci rani da ke cikin Amirka.

Duk da cewa fadar shugaban Amirka sun nesanta Trump da amfani da kalamai marasa dadi, amma kungiyar AU ta bukaci shugaban da ya nemi gafarar kasashen Afirka da Haithi da kuma El Salvador da ya tozartasu.