1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotun Saliyo ta wanke Samura Kamara

Zainab Mohammed Abubakar
May 3, 2023

Babban abokin hamayyar shugaban kasar Saliyo mai barin gado a zabe mai zuwa, ya kawar da wata babbar matsala da ka iya hana shi tsayawa takara.

https://p.dw.com/p/4QrcT
Sierra Leone Samura Kamara, Außenminister
Hoto: Frank Franklin/AP Photo/picture alliance

Samura Kamara, wanda Julius Maada Bio ya doke shi a zaben 2018, yana fuskantar shari'a tun watan Fabrairu bisa zargin cin hanci da rashawa. Magoya bayansa wadanda suka ce lamarin na da nasaba da siyasa, suna fargabar za a yanke masa hukuncin gaggawa wanda zai hana shi shiga zaben da za a yi ranar 24 ga watan Yuni.

Sai dai mai magana da yawun hukumar zaben ya ce, Kamara ya gabatar da bukatarsa na yin takara a hukumance a ranar Litinin, matakin da ya biyo bayan umarnin dage ci gaba da shari'ar tasa har zuwa ranar 14 ga watan Yuli.

A gefe guda kuma, wata babbar kotu a jiya Talata ta ba da umarnin a saki fasfo din Kamara, wanda zai ba shi damar halartar taron kungiyar Commonwealth a Biritaniya, kamar yadda kakakin sashin shari'a Elkass Sannoh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.