Kotun Istanbul ta sake kama ′yan fafutika | Labarai | DW | 21.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Istanbul ta sake kama 'yan fafutika

Wata kotun kasar Turkiya ta bayar a wannan Jumma'a da sammacin sake kamo 'yan fafutikar kare hakkin dan Adam nan su hudu da aka saki ranar 18 ga wannan wata na Yuli bayan da suka share makonni biyu a tsare. 

'Yan fafutikar hudu na daga cikin rukunin 'yan fafutikar kare hakkin dan Adam guda 10 da mahukuntan Turkiyar suka kama ranar biyar ga wannan wata na Yuli a lokacin da suke halartar wani taron samun horo kan harakokin Intanet a tsibirin Büyükada na kusa da gabar ruwan birnin Istanbul inda suka tsare shida daga cikinsu da suka hada da daraktan Kungiyar Amnesty a Istanbul Idil Eser tare da sakin hudu daga cikin mutanen wadanda a yau kotun ta sake neman a kama mata su.

 Mahukuntan Turkiyyar dai na zargin mutanen da aikata babban laifi da suna wata Kungiyar 'yan ta'adda da amma  ba su bayyana sunanta ba.