Kotun Adamawa ta wanke Murtala Nyako | Labarai | DW | 11.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotun Adamawa ta wanke Murtala Nyako

Kotun ɗaukaka ƙara da ke fadar jihar, ta wanke tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako wanda majalisar dokokin jihar ta tsige daga mulki cikin wata Yulin na shekarar ta 2014.

Mai shari'a Jummai Sanki da ta yanke hukuncin a yau Alhamis, ta ce aikin son zuciya da ganin dama ne ƙarara majalisar Adamawan ta yi ta kuma tsige tsohon gwamna .A Saboda hakan nema kotun ta umurci da gwamnati ta gaggauta biyan tsohon gwamna Murtala Nyako duk wasu hakkokinsa na tsawon watanni tara, kafin ƙarewar wa'adinsa.

Majalisar dokokin jihar Adamawan dai a baya, ta kafa hujja tsige Nyakon ne akan laifin yin wadaka da kuɗaɗen gwamnati.