1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Rasha ta daure Navalny a gidan yari na shekaru uku

Abdoulaye Mamane Amadou
February 2, 2021

Wata kotu a Rasha ta yanke daurin gidan yari na shekaru uku da rabi ga madugun adawar kasar Alexei Navalny, bisa samunsa da laifin taka hukuncin kotu da aka yanke masa

https://p.dw.com/p/3omvv
Russland Gerichtsverhandlung Nawalny
Hoto: Moscow City Court/dpa/picture-alliance

Tun daga farko dai alkalai da ke shari'a a kotun sun zargi Navalny ne da taka dokar kotun, bisa yin gaban kansa bayan an masa daurin talala na tsawon shekaru uku a shekarar 2014 a kasar.

Sai dai da yake mayar da martani kan zargin a gabanin hukuncin kotun, Mista Navalny ya musanta zargin karya hukuncin, yana mai bayyana cewa ba zai aminta da daukar laifin ba.

An kama Navalny ne a tsakiyar watan Janeru, bayan ya koma gida sakamakon doguwar jinyar da ya sha a wani asibin da ke nan Jamus saboda shayar da shi wata guba.