Kotu ta dage zaman shari′ar Sheikh Zakzaky | Labarai | DW | 31.03.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta dage zaman shari'ar Sheikh Zakzaky

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta sake dage zaman sauraron shari'ar Shugaban Shi'a a Najeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky har zuwa ranar 25 na watan Mayun bana.

A dazu dazun nan kotun da ke sauraren karar Sheik Ibrahim Yakub Elzazzaky, ta dage zaman shari'ar har zuwa ranar 25 ga watan Mayu na wannan shekarar ta 2021. Wannan na zuwa ne bayan gabatar da manyan shaidu kimanin goma sha biyar da masu shigar da kara na bangaren gwamnatin Kadunan suka gabatar, kan rikicin garin Zaria a tsakanin sojoji da almajiran el-Zakzaky, shekaru shida da suka gabata.

A nasu bangaren lauyoyin da ke kare el-Zakzaky,  sun nunar da cewa dukkanin shaidun da aka gabatar ba su tanadi kwararan hujjoji masu karfi da shari'a za ta iya amfani da su ba, balle har su yi tunanin kare kansu. Sun ce suna cike da fatan za a wankke jagoran na su daga duka zarge-zargen tayar da zaune tsaye da suka yi sanadiyar rayukan mutum sama da dari. Shugaban ya sha musanta zarge-zargen a yayin da magoya bayansa kke ci gaba da fafutukar ganin an sake shi.