Kotu ta dage yanke hukunci ga Ahmed Abba
April 20, 2017Kotun soja ta kasar kamaru ta dage hukuncin da ya kamata ta yanke wa wakilin sashen Hausa na RFI Ahmed Abba dangane da tuhumar da take masa ta hada kai da 'yan ta'adda wajen cutar da kasa. Sai dai lauyansa wanda ake tuhuma Barrister Charles Tchoungang ya nuna mamaki dangane da matakin saboda yau (20.04.2017) ne ranar karshe da doka ta kayyade ta yanke wannan hukunci. Kotun dai ta tsayar da 24 ga watan Afirilu wajen sanar da hukucin da ta yanke wa dan jaridan da ya shafe shekaru 21 a gidan yari.
A ranar 25 ga watan Julin 2015 aka cafke Ahmed Abba a Maroua da ke arewacin kamaru bisa zargin rashin tona asirin 'yan ta'adda da kuma yaba ayyukansu na ta'addanci a cikin rahotannin da ya hada. Sai dai dan jaridar ya yi watsi da duk zarge-zargen da ake masa. Fiye da mutane goma ne aka yanke wa hukuncin kisa a kamaru tun bayan da doka kan ta'addanci ta fara aiki a kasar shekaru biyun da suka gabata.