Kotu ta bada sammacin Donald Trump a Iraki | Labarai | DW | 07.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta bada sammacin Donald Trump a Iraki

A dai-dai lokacin da hankalin duniya ya karkata kan halin da fagen siyasar Amirka ya shiga, zargin kisan daya daga na hannun daman mai fada a ji a rundunar sojan Iran a Iraki.

Wata kotu a Iraki ta bada sammacin kama Shugaba Donald Trump, bisa zarginsa da hannu wajen kisan Abou Mehdi al-Mouhandis, daya daga cikin na hannun daman babban kwamandan sojan Iran na juyin juya hali, Janar Qassem Soleimani a shekarar 2020.

Ko a watan Yunin da ya gabata, Iran ta taba aike da wata wasikar neman sammacin Donald Trump ga hukumar 'yan sandan kasa da kasa ta Interpol, sai da har yanzu hakar Iran din ba ta cimma ruwa ba.

Ayar doka mai lamba 406 ta kundin hukunta laifukan Iraki da kotun ta yi amfani da ita wajen zartar da hukuncin sammacin, ta tanadi hukucin rajamu ne kan duk wani wanda yayi kisa da gangan ga wani dan kasar.