1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi

Uwais Abubakar Idris RGB
March 4, 2023

Bayan an jima ana kai ruwa rana, Kotun koli a Najeriya ta yanke hukunci kan a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi har zuwa karshen wannan shekarar ta 2023.

https://p.dw.com/p/4ODzH
Tsoffin takardun kudin Najeriya
Tsoffin takardun kudin NajeriyaHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci a kan shari'at canjin kudi inda ta umurci babban bankin Najeriya CBN da ya bari a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na Naira dubu 1,000 da 500 da 200 har zuwa ranar 31 ga watan Disamban wannan shekara, abin da ya nuna nasarar da gwamnonin da suka kai kara suka samu a gaban kotun. 

Gwamnan CBN Emefiele da Shugaba Buhari
Gwamnan CBN Emefiele da Shugaba BuhariHoto: Sodiq Adelakun/Xinhua News Agency/picture alliance

Gaba daya dukkanin bukatun da gwamnonin 16 suka gabatar ne a kan wannan sabon tsarin na canjin kudi ta biya masu, abin da ya nuna a fili yadda gwamnonin suka samu gagarumar nasara a kan wannan shari'a ta canjin kudi a Najeriyar.

Murna har baka ga gwamnonin uku da tun farko sune suka fara shigar da karar watau, Nasiru Elrufai na jihar Kaduna da Matawalle na jihar Zamfara da Yahya Bello na ihar Kogi wadanda dukkaninsu sun zo kotun kuma a gabansu aka yanke hukunci.

Duk da narasar da aka samu ana dari-dari a kan matakin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da babban bankin kasar za su dauka ko za su yi biyayya ga wannan umurmi, domin a baya sun ki bin umurnin da kotun ta bayar, abin da masana shari'a suka bayyana hatsarinsa ga kasa da ke bin tafarki na mulkin dimukurdiyya.