Kotu a Masar ta wanke Hosni Mubarak | Labarai | DW | 02.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Masar ta wanke Hosni Mubarak

Kotun daukaka kara a Masar ta wanke tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak daga zargin da ake yi masa da hannun wajen aikata kisa a kan masu zanga-zaga a shekara ta 2011.

A shekara ta 2012 aka yanke wa Mubarak hukuncin daurin rai da rai a gidan kurkuku, saboda lafin kafin daga bisani wata kotun ta soke shari'ar.Yanzu haka dai Hosni Mubarak din dan shekaru 87 da haifuwa wanda ya kwashe sama da shekaru 30 a kan gadon muli na kwance yana jinya a  asibiti.