Hosni Mubarak tsohon shugaban kasar Masar kana tsohon babban hafsan sojoji wanda ya yi mulki daga shekarar 1981 zuwa shekara ta 2011.
Juyin-juya hali da ya ritsa da wasu kasashen Larabawa ya yi sanadiyyar kawo karshen gwamnatin Mubarak a shekara ta 2011, kuma daga bisani ya gurfana a gaban kotu bisa tuhumar ya dauki matakin da ya saba doka kan masu zanga-zanga.