Kotu a China ta yankewa Jihua hukunci | Labarai | DW | 04.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a China ta yankewa Jihua hukunci

Kotu a kasar China ta yankewa wani na kusa da tsohon shugaban kasar Hu Jintao daurin rai da rai sakamakon samun sa da laifin cin hanci da karbar rashawa.

Ling Jihua ya fuskanci hukuncin daurin rai da rai

Ling Jihua ya fuskanci hukuncin daurin rai da rai

Kamfanin dillancin labarai na Chinan Xinhua ya ruwaito cewa kotun da ke zamanta a birnin Tianjin, ta samu Ling Jihua da laifin almundahana da kudade da kuma yin amfani da matsayinsa ta hanyar da bata dace ba. Mai shekaru 59 a duniya, Jihua ya rike mukamin kwamitin lura da al'amura na jam'iyar communist da ke mulki a kasar, kana kuma shi ne shugaban ma'aikata na gwamnatin tsohon shugaba Hu Jintao. Tun a watan Maris na 2012 ne Jihua ya fara fuskantar zargi bayan da dansa ya mutu sakamakon hadarin mota da ya rutsa da shi a wata mota mai dankaren tsada, abin da ya sanya mutane suka fara tunanin yadda aka yi dansa ya mallaki wannan mota. A watan Satumba na 2012 ne kuma Jihua din ya rasa mukaminsa bayan da Shugaba Xi Jinping ya zama sabon shugaban kasa a China.