Kotu a Birtaniya ta kori karar Najeriya | Labarai | DW | 23.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Birtaniya ta kori karar Najeriya

Najeriya ta shigar da karar ne kan badakalar kudi da kamfanonin Shell da ENI suka ce sun biya gwamnatin baya. Sai dai kotun Birtaniya ta yi watsi da karar domin wata kotun Italiya na ci gaba da sauraren wannan karar.

Wata kotu a birnin Landan ta yi watsi da karar da gwamnatin Najeriya ta shigar a gabanta tun a shekara ta 2018, dangane da badakalar mallakar wuraren hakar man fetur da kamfanonin Shell da Eni na kasar Italiya suka ce sun cika duk wasu ka'idojin da suka kamata na samun damar hakar danyan mai tun a shekara ta 2011.

Gwamnatin ta Najeriya ta shigar da karar ne a wata kotun kasuwanci a kasar ta Birtaniya kan badakalar ta dalar Amirka sama da miliyan dubu guda da kamfanonin suka ce sun biya gwamnatin baya wanda kuma gwamnati mai ci yanzu ta ce damfarar su aka yi.

Kotun ta ce ba za ta iya ci gaba da sauraren karar ba domin wata kotu a birnin Milan na Italiya na ci gaba da sauraren irin wannan karar, yunkurin da bai yi wa hukumomin Najeriya dadi ba, inda a dayan bangaren kamfanin hakar man na Shell ya yi na'am da wannan mataki.