Koriya ta Kudu za ta afka wa ta Arewa | Labarai | DW | 10.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Kudu za ta afka wa ta Arewa

Koriya ta Kudu za ta ta afkawa Koriya ta Arewa, bayan wata sanarwar da Koriya ta Arewar ta fitar kan shirinta na farwa wani tsibiri na kasar Amirka.

Kasar Koriya ta Kudu ta ce a shirye ta ke da ta afkawa makwabciyarta Koriya ta Arewa, bayan fitowar sanarwar Koriya ta Arewar kan shirinta na farwa tsibirin Amirka na Guam. Wani kakakin manyan hafsoshin Koriya ta Kudun, ya ce a duk lokacin da suka hango alamun hari daga Koriya ta Arewan, to la budda za su kai mata hari ba tare da wata-wata ba.

A baya dai Koriya ta Arewa ta yi barazana kan yankin na Guam, bayan kafa wani sansanin kare kai daga harin makami mai linzami da Amirka ta yi shekaru hudun da suka gabata.