Koriya ta harba makami mai linzami | Labarai | DW | 30.01.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta harba makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami wanda shi ne mafi girma tun bayan wanda ta harba a shekara ta 2017.

Makamin mai linzamin wanda Koriya ta harba daga Jagang inda ta saba harbawa da ke a gabar tekun gabashin kasar, ya yi gudun kilomita 800 a cikin mitoci 30 daga wurin da aka harbashi a tafiyar kololuwa ta kilomita dubu biyu kafin ya fada a cikin tekun Japan. A cikin wata sanarwa da ya bayyana shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae In ya ce Koriya ta Arewa na nesa da yin amana a kan bukatar kasashen duniya na yin watsi da gwaje-gwajen na makaman nukilya kafin ya bayana kiran taron gaggawa na tsaro na kasarsa. Wannan gwaji wanda shi ne na bakwai tun farkon wannan shekara na zuwa ne a daidai lokacin da China kawarta ke shirin karbar bakwancin wasannin Olympic na sanhi hunturu, yayin da Koriya ta Kudu za ta gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Maris da ke tafe.