1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami

March 27, 2023

Hukumomi a kasashen Japan da kuma Koriya ta Kudu sun ce, Koriya ta Arewa ta harba wasu makamai biyu da ake kyautata zaton makamai masu linzami ne zuwa gabar gabashin ruwanta.

https://p.dw.com/p/4PHLF
Hoto: KCNA/REUTERS

Kasar Koriya ta Kudu ta ce ta bi diddigin makaman da makwafciyarta Arewa ta harba. Sai dai yayin da take tabbatar da hakan, kasar Japan ta ce makaman sun sauka ne a wajen yankin tattalin arzikinta.

Kasashen biyu dai sun yi Allah wadai da matakin makwafciyarsu, kana suka ce za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko ta kwana yayin da suke sa ido kan ayyukan Koriya ta Arewa.

Koriya ta Kudu ta kuma yi ikrarin ci-gaba da karfafa alaka da Amirka. A cikin wannan shekarar, kasar Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami kimanin 20 a wani mataki na tursasawa Amirka amincewa da matsayinta kan makaman nukiliya tare da neman kulla yarjejeniya domin janye takunkuman da aka kakaba mata.