Koriya ta Arewa: Harba makami kan Japan | Labarai | DW | 04.10.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa: Harba makami kan Japan

A karon farko cikin shekaru biyar, kasar Koriya ta Arewa ta harba makami mai linzami kan Japan; lamarin da ya tilastawa Japan dakatar da dukkan jiragen kasa a tsibirin Hokkaido da Aomori.

Japan ta gargadi mazauna yankunan arewa maso gabashin kasar ta su kauracewa yankin inda daga bisani gwamnatin kasar ta ce makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta harba ya sauka ne a kan tekun Pacific.

Firanministan Japan Fumio Kishida ya yi Allah wadai da lamarin ya na bayyana hakan a matsayin ganganci.

Ita ma dai Amirka ta kakkausar suka kan Koriya ta Arewa, ta mai cewa abu ne mai matukar hadari a harba makamin mai cin dogon zango kan Japan. Koriya ta Arewa dai ta yi gwajin makami mai Linzami kimanin sau 20 a wannan shekarar yayin da shugaba Kim Jong Un ya sha alwashin fadada makaman nukiliyarsa da kuma kin koman kan yarjejeniyar nukiliya da Amirka.