Kona ofishin jakadancin Saudiya a Iran | Labarai | DW | 20.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kona ofishin jakadancin Saudiya a Iran

Jagoran addinin Islama na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi tir da harin da wasu da suka fusata suka kai a ofishin jakadancin Saudiya da ke Tehran babban birnin kasar.

Jagoran addinin Islama na Iran Ayatollah Seyed Ali Khamenei

Jagoran addinin Islama na Iran Ayatollah Seyed Ali Khamenei

Khamenei ya bayyana harin da cewa ya tozarta kasarsa da ma addinin Musulunci. Khamenei wanda ya bayyana haka a shafinsa na Internet, ya kuma yabawa dakarun juyin-juya hali na kasar dangane da tsare mayakan ruwa na Amirka na wani dan lokaci da suka yi a makon da ya gabata, sakamakon keta kan iyakar ruwan kasar ta Iran da suka yi. A ranar biyu ga wannan wata na Janairu da muke ciki ne dai wasu masu zanga-zanga domin nuna fushinsu dangane da zartas da hukuncin kisa a kan shahararren malamin addinin Islamar nan mabiyin mazhabar Shi'a dan asalin kasar ta Saudiya, Ayatollah Nimr Baqir Nimr da mahukuntan Saudiyan suka yi, suka kai hari a kan ofishin jakadanicn Saudiyan da ke Tehran babban birnin kasar ta Iran inda suka cinna masa wuta.