Komitin Syria ya fara sauraren mutanen da a ke tuhuma da hannu a mutuwar Hariri | Labarai | DW | 10.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Komitin Syria ya fara sauraren mutanen da a ke tuhuma da hannu a mutuwar Hariri

A wani mataki na shaidawa dunia cewa ba da wasa su ke ba, hukumomin Syria sun bullo da dokar hana hita daga kasar, ga dukan mutanen da binciken komitin Majalisar Dinkin Dunia, ya gudanar ya ambaci sunayen su a cikin mutuwar Raffik Hariri.

Komitin binciken da Syria ta girka ne, ya dauki wannan mataki jim kadan bayan, ganawar da a ka yi tsakanin sakataran kungiyar hadin kan Larabawa Amr Musa, da shugaban Syria Bashar Al Assad.

Yau ne ma shugaba Ál Assad ke gabatar da jawabi, domin bayyana matsayin gwamnatin sa, a kan wannan al´amari.

Shi ma sakatare Janar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan ya kai ziyara aiki a Saudiyya, inda ya kiri Sarki Abdallah da ya yi anfani da kimar sa, da kuma mutuncin sa, domin shawo kan hukumomin Syria, su bada hadinkai a gano haske a kan kissan tsofan Praministan Labanon.