Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A Jamhuriyar Nijar, kayataciyyar kokowar gargajiya karo na 42 ta gudana a Yamai inda Issaka Issaka na jihar Dosso ya zama sabon sarki, bayan da ya samu nasara a kan Aibo Hassan na jihar Maradi.
Mamakon ruwan saman da ake tafkawa a jamhuriyar Nijar ya yi sanadiyar rayukan mutane sama da 190 yayin da ibtila'in ya haifar da babbar asara ga wasu da yawansu ya haura dubu dari uku.
Gwamnati a Jamhuriyar Nijar ta ce mamakon ruwan sama ya hadasa mummunan ambaliyar da a ciki mutane 192 suka mutu, wasu fiye da dubu 260 suka rasa gidajensu.
Sabon takun saka ya kunno kai tsakanin gwamnatin Nijar da kungiyar malaman jami’o’i da ma ta dalibai kan garambawul da aka yi wa tsarin aikin jami’o’in kasar, lamarin da suka ce zai haifar da komabaya ga harkar ilimi.
Mahukuntan Jamhuriyar Nijar, sun kudiri aniyar daukar matakai domin kare rayukan yara kanana da ke makarantun reno wato Nursery. Wannan na zuwa ne bayan gobara ta lakume rayukan daliban firamare a jihar Maradi.