Kokarin warware rikicin Gabas ta Tsakiya | Labarai | DW | 04.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin warware rikicin Gabas ta Tsakiya

Ministan harkokin wajen Siriya Walid Muallem ya isa kasar Iran don fara tattaunawa da takwarorinsa kan halin da kasar ta Siriya da ma yankin gabas ta tsakiya ke ciki.

Kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA ya ce mukaddashin ministan harkokin wajen Rasha Mikhail Bogdanov da kuma mataimakin ministan harkokin wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian ma dai za su hallarci tattaunawar da za a yi.

Yayin zaman da za su yi dai, ana sa ran za wakilan kasashen uku su yi kokarin shata hanyoyin da za a bi na samar da zaman lafiya a Siriya da Yemen da kuma wasu kasashen da ke fama tashin hankali a yankin gabas ta tsakiya.