1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun dukufa don ganin bayan rikicin Zamfara

August 17, 2018

A wani abun da ke zaman gagarumin ci-gaba a bangaran jami’an tsaro na Tarrayar Najeriya, babban hafsan sojin sama na kasar ya ce an yi nasarar kakkabe 'yan ina da kisan da suka addabi al'umma a jihar Zamfara.

https://p.dw.com/p/33KRc
Nigeria Soldaten
Hoto: AFP/Getty Images

Darururwan mutane ne dai suka yi asarar rayuwarsu bayan barazana ga harkar noma da kasar take takama da shi, duk kuma a sakamakon ayyukan 'yan ina da kisan da suka addabi jihar ta Zamfara da ke sashen arewacin Tarrayar Najeriya. To sai dai kuma daga dukkan alamu wani sabon hobbasa a bangare na jami'an tsaron Tarrayar ta Najeriyar ya fara nuna alamun nasara da kuma magance matsalar barayin shanu da suka hana ruwa gudu a yankin. Kuma a fadar babban hafsan sojin saman na Najeriya Air Marshal Sadiq Abubakar, akwai alamun nasara da nufin kai karshen barazanar da ke zaman barazanar tsaro mafi girma a cikin kasar a halin yanzu.

Kamerun Symbolbild Soldaten im Norden ARCHIV
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

An dai dauki lokaci ana kallon tashi da lafawar rikicin da kan tada hankulan kauyuka dama kisa irin na kan mai uwa da wabi a garuruwa da dama a jihar. Har ma ana zargin rikidewar yanayin da Boko Haram. To sai dai a fadar Air Marshal Sadiq din babu wata alama da ke iya danganta abun da ke faruwa a zamfaran da Boko Haram.

Tarayyar Najeriyar dai na shirin fuskantar zabe a nan gaba kuma rikicin rashin tsaron na iya illa ga makomar zaben da ma watakila makomar kasar baki daya, hujjar kuma da a cewar Air Marshal Sadiq babu gudu babu ja da baya ga tabbatar da kare zubda jini a zamfara dama makwabtan na Zamfara. Abun jira a gani dai na zaman nasarar ayyukan jami'an tsaron a kokarin sake dasa wata damba ta zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma a kasar.