1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin shawo kan rikicin siyasa a Libanon

Ibrahim SaniNovember 15, 2007
https://p.dw.com/p/CHYB

Sakataren Majalisar ɗinkin duniya, Mr Banki Moon ya isa ƙasar Libanon, a ƙokarin da ake na samo bakin zaren warware rikicin siyasa a ƙasar.A lokacin ziyarar, Mr Banki Moon zai gana da jami´an Gwamnatin ƙasar da kuma na ´Yan adawa.Ziyarar ta Banki Moon ta zo ne, saura kwanaki ƙalilan a gudanar da zaben shugaban ƙasar.Libanon dai ta faɗa rikicin siyasa ne, bayan da ´Yan Majalisar dokoki suka gaza cimma madafa ne kan wanda zai gaji Mr Emele Lahoud ne da wa´adinsa, ke ƙarewa a ranar 24 ga watannan. ´Yan adawa na ƙasar sun zargi Mr Lahoud ɗin ne, a matsayin ɗan koren ƙasar Syria.Hakan shiya haifar a cewar rahotanni, su ke muradin maye gurbinsa da mai matsakaicin ra´ayi.