Kokarin samun zaman lafiya a Siriya | Labarai | DW | 03.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin samun zaman lafiya a Siriya

Mukaddashin ministan harkokin wajen Siriya Faisal Mekdad ya yi watsi da maganganun da ake yi na samun sauyin gwamnati a kasar da nufin kawo karshen rikicin da ake yi.

Mr. Mekdad ya bayyana hakan ne bayan da ya isa birnin Tehran na kasar Iran domin tattaunawa da hukumomin kasar kan lamarin da ya danganci halin da ake ciki a kasar ta Siriya.

Masu aiko da rahotanni suka ce mukaddashin ministan harkokin wajen Siriya din ya ce yanzu haka suna kokari ne na ganin sun an hade kan kasar wajen guda da nufin dinke barakar da ke akwai sabanin rade-radi da ake na saukar Shugaba Assad daga gadon mulki.

Wannan matakin da suka dauka inji Mr. Mekdad zai kunshi damawa da wasu bangarori na mutanen kasar duka dai da nufin ganin an samu zaman lafiya sai dai wasu kasashen yamma na son ganin an samu sauyin shugabanci a kasar.