Kokarin neman mafita a Najeriya
September 28, 2017Har ya zuwa yanzun dai babbar matsala a tsakanin 'yan mulki dama talakawa a Najeriyar dai na zaman amsa tambaya muhuimmiya guda game da gamsuwa da yadda tsarin kasar ke tafiya a lokaci mai nisa. Duk da cewar dai an doshi shekaru har 60 ana faduwa ana sake tashi, hankoro na kuma kara karuwa tsakanin masu neman da a ware da masu tunanin sake tsarin da muryarsu ke kara karfi cikin kasar a halin yanzu.
Manyan 'yan boko da 'yan siyasar na Najeriya sun hadu suka yi tunanin cewar akwai bukatar a samu mafita ga halin da kasar take cki a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Najeriya General Yakubu Gowon. Farfesa Jerry Gana dai na zaman daya a cikin wakilai daga yankin arewa ta tsakiya a cikin wata tattaunawa da kungiyar tattaunawa da ci gaba mai zaman kan ta da ke a Abuja ta kai ga shiryawa da nufin nazarin bukatu na 'yan kasar sannan kuma da neman hanyar dorawa cikin kokarin ginin kasar da ke neman rushewa.