1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin magance matsalar tattalin arzikin Najeriya

Ubale MusaMarch 22, 2016

A karon farko tun bayan hawansu mulki, gwamnonin Najeriya da kuma sabuwar gwamnatin kasar na nazarin samun mafita ga matsalar tattalin arzikin kasar.

https://p.dw.com/p/1IHDv
Yomi Osinbajo und Muhammadu Buhari (Nigeria APC)
Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi OsinbajoHoto: DW/Uwais Abubakar Idris

Sun dai share tsawon wattani kusan tara suna bundun bundum, amma kuma har yanzu suna tsakiyar ruwa ga sabbabin yan mulkin Tarrayar Najeriya da suka yi alkawarin sauyi amma kuma ke fama da matsananci na rashin kudi a halin yanzu, abun kuma da ya dauki hankalin mammalakan kasar ta Najeriya da suka share wunin wannan rana ta Litinin suna nazarin mafitar matsalar da ke barazana ga alkawarinsu na sauyi sannan kuma ke neman maida kasar can baya.

Kama daga kasashe irin nasu India, ya zuwa Kwarraru a sassa daban-daban na cikin gida dai gwamnonin kasar 36 da ministocin da ke da ruwa da tsaki da harkokin kudi da tattalin arzikin kasar karkashin jagorancin mataimakain shugaban kasar Yemi Osinbajo, sun shafe tsawon wunin wannan rana suna saurare na dabaru a kokari na fidda kasar daga cikin halin da ta shiga a halin yanzu.

Alhaji Kashim Shettima
Gwamnan jihar Borno Alhaji Kashim ShettimaHoto: DW/U. Musa

An dai tabo maganar noma da kuma ma'adinai, duk dai da nufin samo sauyi daga man fetur din da daga dukkan alamu ke neman kai kasar sannan ya baro al'ummarta miliyan170 bayan kusan shekaru 40 ana danyen ganye. Farfesa Abba Gambo dai na zaman daya a cikin masana a harkokin noma na kasar da kuma suka kalli idon shugabanni na siyasa ta kasar suka ce musu sake lale na zama na wajibi in har ana bukatar kaiwa ga gaci a kasar.

za a dai a share tsawon kwanaki biyu ana nazari na sabbabi na dabaru kamun daga baya akai ga kafa kwamitoci na kwararru da za su kafa dan ba na aiwatar da daukaci na dabarun taron da ke zaman irin sa mafi girma ga gwamnatin kasar. Abun jira a gani dai na zaman mafita ga yan mulkin da ke tsakanin iya karkatar da akalarsu zuwa wasu sassan a kankane na lokaci da kuma fuskantar dawowa daga rakiyar talakawan da ke zaman jiran sauke alkawarin sauyi na kasar.