1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kyautata harkar man fetir a Najeriya

Uwais Abubakar Idris MA
March 29, 2018

A Najeriya majalisar dokokin kasar ta amince da kudurin dokar sake wa sashin man fetir na kasar fasali bayan kwashe shekaru ana takaddama a kan dokar.

https://p.dw.com/p/2vDdV
Nigeria Port Harcourt Arbeiter auf Plattform Ölförderung
Daya daga cibiyoyin tace mai mallakin gwamnatin NajeriyaHoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Wannan sabon yunkuri ne da Najeriya ta kwashe fiye da shekaru 17 ana fusknatar jan kafa a kan kudurin dokar da nufin kyautata daukacin sashin man fetir din kasar da ya kasance mai samar da fiye da kashi 90 na kudadden shigan kasar.

Kudurin dokar da majalisar ta sake wa fasali daga wacce aka faro tun da farko, ta samar da sanya haraji na kashi 5 a kan duk man fetir din da aka sayar a cikin gida tare ma da samar da damar kafa hukuma ta musamman don kula da yadda ake tafiyar da harkokin man fetir, da nufin kawar da zargin sama da fadi da cin hanci a wannan sashi da ya zama nonon tatsa a Najeriyar.

Nigeria Tankstelle in Lagos
Hoto: AFP/Getty Images/P. U. Ekpei

Tun da dadewa ake takaddama a kan yadda ake tafiyar da harkar man Najeriyar da a shekarun baya ta zama babbar hanyar ruf da ciki a kan dukiyar Najeriyar. Ga masu kula da harkokin man fetir din na bayyana wannan mataki da muhimmin ci gaba. 

 

Abin jira a gani shi ne amincewa da sanya hannu kan a dokar daga bangaren zartaswa, da ma tasirin da zai iya yi wajen sake fasalin harkar man fetir din Najeriyar da ke cike da matsaloli, kama daga yankin da ake samar da shi ya zuwa na cin hanci da rashawa.